Direba ya kashe dan Adaidaita Sahun da ya gogar masa mota a Legas

Direba ya kashe dan Adaidaita Sahun da ya gogar masa mota a Legas

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas, ta ce tuni ta dukufa wajen gudanar da bincike na neman cafke wani direban mota da ya kashe wani matukin babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Adaidaita Sahu, Bassey Anieta a unguwar Shitta- Surulere.

Wannan mummunan lamari ya auku a yayin da sa'insa ta barke tsakanin direban motar da kuma marigayi Anieta wanda bai wuce shekaru 26 ba a duniya. Ana zargin cewa laifin matashin bai wuce tsautsayin masu ababen hawa ba inda ya dan gogi jikin motar direban da Adaidaita Sahunsa.

Ba tare da aune ba a yayin yunkurinsa na neman sulhu, direban motar wanda a halin a yanzu ya yi aron kafar kare, ya hau dokin zuciya bayan fitowar sa daga mota inda ya yi amfani madaurin tayar mota wato 'Wheel Spanner' wajen yiwa marigayi Anieta jina-jina.

Kamar yadda manema labarai na jaridar Sahara Reporters suka ruwaito, an yi gaggawar garzaya wa da marigayi Anieta zuwa asibitin kurkusa, inda gabanin ya gabata a gaban likitoci ya ce ga garin ku nan a sakamakon jini da ya rika kwaranya ta hanci da baki.

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da binciken jami'an tsaro ya yi zurfin gaske, kakakin 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya bayar da tabbacin wannan rahoto tare da zargin mashaidan wannan ta'addanci da nuna halin ko in kula wajen bai wa direban motar damar arcewa.

KARANTA KUMA: Tafiya kasar Indiya: Zakzaky ya ki hawa jirgin fadar shugaban kasa

A can birnin Kanon Dabo kuma, hukumar 'yan sandan jihar ta yiwa masu Adaidaita Sahu kashedi na tabbatar da kiyaye duk wata doka da hukumomi masu ruwa da tsaki gami gwamnati suka shimfida da manufar kare al'umma da kuma dukiyoyin su.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel