2023: Yankin arewa za ta zama butulu idan har bata mika wa kudu mulki ba – Shehu Sani

2023: Yankin arewa za ta zama butulu idan har bata mika wa kudu mulki ba – Shehu Sani

Tsohon Sanata mai wakiltan Kaduna a majalisar dokoki ta takwas, Shehu Sani, ya caccaki wadanda ke da muradin ganin arewa ta riki mulki fiye da shekarar 2023.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Sani yace arewa za ta zama butulu idan har taki mika mulki ga yankin kudu ayan cikar wa’adin shugabancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu.

Legit.ng ta tattaro cewa Sani wanda ke martani akan kira da Gwamna Nasir El-Rufai yayi kwana nan kan soke batun rarraba mulki, yace zai zama rashin adalci ga arewa idan har ta ci gaba da rikon mulkin Najeriya bayan shekaru takwas.

Gwamna El-Rufai ya nemi a daina rabon mukaman siyasa ga yankuna, cewa akwai bukatar sake duba lamarin da kuma soke rabon domin a ba da damar duba kokarin mutum.

KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya ya dawo da $800 da ya tsinta a kasar Saudiyya

Yace ba zai yiwu Najeriya ta ci gaba akan wannan tarba na rabon mukamai zuwa ga yanki nko asali ba, inda ya bayyana hakan a matsayin shinge ga daidaiton siyasa.

Da yake martani ga furucin El-Rufai a lokacin da ya kai ziyarar Sallah ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa a ranar Litinin, 12 ga watan Agusta, Sani ya bayyana cewa yankin kudu, musamman kudu maso yamma, sun yi duk kokarinsu domin ganin Buhari yayi nasara a 2015.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel