Wani dan Najeriya ya dawo da $800 da ya tsinta a kasar Saudiyya

Wani dan Najeriya ya dawo da $800 da ya tsinta a kasar Saudiyya

Abdullahi Suleiman, wani mahajjacin Najeriya wanda ke gudanar da aikin hajji yanzu haka a kasar Saudiyya, ya tsinci wasu makudan kudade har $800 sannan ya mayar das hi ga jami’an hukumar aikin hajji.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Suleman, wanda ya kuma kasance direban sarkin Keffi a jihar Nasarawa, Alhaji Shehu Chindo Yamusa, ya dawo da kudin ga hukumar aikin hajji na jihar Nasarawa a kasar Saudiyya.

Legit.ng ta tattaro cewa Amirl hajji kuma sarkin Lafia, Alhaji Sidi Dauda Bage, ya karrama mahajjacin akan aikin alkhairi da yayi.

Suleiman yayi godiya ga sarkin akan aikin alkhairi da karamcin da ya nuna.

Sarkin ya kuma bayyana cewa ya yi jawabi ga talakawansa akan su kasance masu aikin alkhairi a duk inda suka tsinci kansu, cewa cuta bai da amfani.

KU KARANTA KUMA: Burinmu ya cika kan shugabanmu El-Zakzaky – Kungiyar Shi'a

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa mai martaba Sarkin Daura, Umar Faruq Umar, ya roki Ubangiji ya cigaba da kare shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sarkin ya yi wa shugaban kasar addu’a ne a Ranar da Musulman Duniya ke bikin Sallah. Mun ji cewa Sarkin ya yi wannan addu’a ne a lokacin da a ka yi sallar idi a filin Kofar Arewa da ke cikin Garin Daura a jihar Katsina. An yi sallar ne a da safiyar Ranar Lahadi, 11 ga Watan Agusta, 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel