Burinmu ya cika kan shugabanmu El-Zakzaky – Kungiyar Shi'a

Burinmu ya cika kan shugabanmu El-Zakzaky – Kungiyar Shi'a

Kungiyar yan uwa Musulmai na Shi'a ta bayyana cewa abin da ta dade tana gwagwarmaya gani ya tabbata, bayan fitar jagoranta, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky kasar Indiya domin neman magani.

A ranar Litinin, 12 ga watan Agusta ne Sheikh Ibrahim Zakzaky ya tafi kasar Indiya don neman magani kuma ya tashi ne daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, zuwa Indiya.

Kungiyar ta ce ta jingine duk wata zanga-zanga a yanzu saboda abin da ta dade tana gwagwarmaya akai ya tabbata.

Rahotanni sun kawo cewa malamin zai fara yada zango ne a birnin Dubai, kafin daga bisa ya wuce kasar Indiya, inda zai yi jinya a asibitin Medanta.

Idan za ku tuna a baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kungiyar IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya tashi zuwa kasar Indiya daga babban filin Nnamdi Azikwe dake Abuja domin jinya biyo bayan belin da kotun jihar Kaduna ta bashi a makon da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Jega ne ya soke rajistar Jam’iyyar PRP a 2014 – Inji Balarabe Musa

Alkalin kotun jihar Kaduna ya baiwa El-Zakzaky damar fita kasar Indiya inya bisa ga bukatar lauyan kungiyar IMN, Femi Falana SAN.

Kwararrun likitoci da suka gudanar da bincike kan koshin lafiyar shugaban kungiyar masu akidar Shi'a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El- Zakzaky da kuma mai dakin sa Zeenatu, sun nemi a yi gaggawar fidda su kasar waje domin samun ingatacciyar kulawa ta nema masu magani.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel