Da duminsa: Zakzaky ya tafi Indiya jinya

Da duminsa: Zakzaky ya tafi Indiya jinya

Shugaban kungiyar IMN wanda akafi sani da yan Shi'a, Sheik Ibrahim El-Zakzaky, ya tashi zuwa kasar Indiya daga babban filin Nnamdi Azikwe dake Abuja domin jinya biyo bayan belin da kotun jihar Kaduna ta bashi a makon da ya gabata.

Alkalin kotun jihar Kaduna ya baiwa El-Zakzaky damar fita kasar Indiya inya bisa ga bukatar lauyan kungiyar IMN, Femi Falana SAN.

Kwararrun likitoci da suka gudanar da bincike kan koshin lafiyar shugaban kungiyar masu akidar Shi'a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El- Zakzaky da kuma mai dakin sa Zeenatu, sun nemi a yi gaggawar fidda su kasar waje domin samun ingatacciyar kulawa ta nema masu magani.

Kungiyar kwararrun liktocin daga kasar Birtaniya da ta ziyarci El Zakzaky da ke tsare a hannun hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS, ta hadar da likitan ido, likitan zuciya da kuma kwararren likitan 'kashi.

Gwamnatin tarayya ta haramta kungiyar yan Shi'a a Najeriya wadanda akafi sani da mabiya EL-Zakzaky.

A cikin mako daya kacal, an yi asarar akalla rayuka 20 sakamakon rikici tsakanin yan Shi'an da yan sanda a birnin tarayya Abuja inda suke gudanar da zanga-zangan bukatar sakin shugabansu.

KU KARANTA: Komai ya kankama domin shillawar Zakzaky Indiya

Da duminsa: Zakzaky ya tafi Indiya jinya

Da duminsa: Zakzaky ya tafi Indiya jinya
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel