Jega ne ya soke rajistar Jam’iyyar PRP a 2014 – Inji Balarabe Musa

Jega ne ya soke rajistar Jam’iyyar PRP a 2014 – Inji Balarabe Musa

Mun samu labari cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Balarabe Musa, ya yi magana bayan tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya shiga jam’iyyar PRP mai adawa a Najeriya.

Malam Balarabe Musa ya bayyana cewa Attahiru Jega ne wanda ya sokewa jam’iyyar adawar ta PRP rajista a 2014 lokacin ya na shugabantar hukumar zabe mai zaman kan ta watau INEC.

Balarabe Musa ya tunawa jama’a cewa Attahiru Jega ya ki amincewa da PRP a matsayin jam’iyya a lokacin ya na shugabantar hukumar zabe duk da kotu ta bada umarni a tabbatar da jam’iyyar.

A lokacin da tsohon shugaban jam’iyyar na PRP ya karbi ziyarar bikin sallah daga Sanata Shehu Sani a gidansa da ke Kaduna, ya bayyana cewa ya yi farin ciki da jin cewa Jega zai shiga PRP.

“Lokacin da shugaban jam’iyya, Alhaji Falalu Bello, ya fada mani cewa Jega ya na sha’awar shigowa PRP, sai na yi maraba da shi, ina mai cewa kofar mu a bude ta ke ga kowa ya shigo.”

KU KARANTA: Jega ya shiga siyasa dumu-dumu bayan ya zama 'Dan jam'iyyar PRP

Dattijon ya cigaba da cewa:

“Bayan mako guda ko biyu, sai na ji labari a jarida cewa Jega ya shigo jam’iyya. Na yi murna domin na san zai yi mana amfani. Amma dole mu bi a hankali, mu yi hattara a kan wanene Jega?”

“A lokacin da Jega ya ke rike da INEC ne a ka sokewa PRP rajista wanda mu ka yi ta gwagwarmaya. Mu ka je kotu, a ka dawo da mu, amma a ka gagara bin wannan umarnin da kotu ta bada.”

Musa ya ce sai ga shi yau, Jega ya dawo ya shiga tafiyar PRP duk da abin da ya yi mata a baya. Shugaban dattawan jam’iyyar ya ce ba za su kori Farfesan ba, amma ya kamata su yi hattara da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel