Jami'ar Bayero dake Kano ta samu lasisin kafa gidan Talabijin

Jami'ar Bayero dake Kano ta samu lasisin kafa gidan Talabijin

Shugaban sashen ilimin digirin gaba na jami'ar Bayero BUK, Farfesa Umaru Pate ya bayyana cewa hukumar yada shirye-shiryen Najeriya ta baiwa jami'ar lasisin kafa gidan talabijin domin horon dalibai.

Farfesa Pate yace: "An bamu lasisin watsa shirye-shirye wanda zamu iya amfani da shi wajen ilmantarwa da kuma kasuwanci, saboda haka na zuwa shekara mai zuwa da yiwuwan mu kaddamar da watsa shirye-shirye.

Ya bayyana Daily Trust cewa jami'ar a yanzu ta nada gidan rediyo mai kayayyakin aikin zamani amma har yanzu basu kaddamar da ita ba.

Yace: "A yanzu haka muna saye-sayen kayayyakin kawata wajen domin tabbatar da cewa dalibai sun samu horo mai kyau."

"Baya ga haka, muna da dakin ajiye kamfutoci wanda muka shirya domin tabbatar da cewa dalibai sun samu horon iya amfani da na'urorin zamani."

Ya ce gidan talabijin ba kawai ilmantar da dalibai zai yi ba, amma zai taimaka wajen tallata jami'ar a fadin duniya.

A bangare guda, An kori daliban Jami'ar Bayero ta Kano, BUK guda 24 mafi yawancinsu 'yan ajin karshe daga jami'ar bayan an gano sun gabatar da takardun karatun bogi yayin shiga jami'ar tun da farko.

Sanarwar ta fito ne daga mai magana da yawun jami'ar, Lamara Garba da ya ce mahukunta makarantar sun amince da korar daliban ne yayin taron majalisar jami'ar karo na 374 da aka gudanar ranar Laraba 31 ga watan Yulin 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel