Mun fara binciken gobarar Takwa Bay - Inji Rundunar ‘Yan Sanda

Mun fara binciken gobarar Takwa Bay - Inji Rundunar ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke Legas ta ce za ta fara gudanar da bincike a kan abin da ya jawo wata gobara da ta ci ran Bayin Allah a wata Unguwa da ke kira Takwa Bay kwanaki.

Wannan gobara da ta barke a wannan karamar Unguwa ta Takwa Bay ta yi sanadiyyar mutuwar wasu Yara ‘yan gida daya har su biyar a jihar. Yanzu an fara bincike a game da wannan hadari.

Jami’an ‘yan sandan da ke binciken irin wadannan munanan hadari da ke Unguwar Yaba a jihar Legas sun fara tattara hujjoji da bayanai game da wannan gobara domin bada cikakken rahoto.

KU KARANTA: Takarar Gwamna ta raba kan ‘Yan gida daya a Kogi

Hakan na zuwa ne bayan babban Jami’in ‘yan sanda na Legas, Zuabairu Muazu, ya bada umarni a binciki lamarin. A Ranar Lahadin da ta gabata ne Dakarun ‘yan sanda su ka fara cika umarnin.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Legas, Bala Elkana, ya tabbatarwa jama’a aukuwar wannan gobara a Ranar Larabar da ta wuce watau 7 ga Watan Agusta, 2019. Abin ya faru ne da safiyar ranar.

Kamar yadda jami’an tsaron su ka bayyana, wannan annoba ta gobara ta kashe wasu yara ‘yan gida daya. Kafin makon na jiya, an samu wata gobara da ta kashe rai da dukiya a Kauyen Abagbo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel