Wani matashi ya bude wuta a masallacin Al-Noor

Wani matashi ya bude wuta a masallacin Al-Noor

A ranar Asabar, jami'an tsaro sun damke wani matashi mai suna, Philip Manshaus, yayinda ya budewa masallata wuta a Masallacin Al-Noor dake Oslo, babbar birnin kasar Norway inda mutum daya ya jikkata.

Daga baya, jami'an tsaro sun ga gawar wata mata a cikin gidansa.

Shugaban masallacin, Irfan Mushtaq, ya bayyanawa manema labarai cewa wani masallaci mai shekaru 75 ne ya jikkata cikin dukkan masallatan.

Yace wani matashi sanye kayan yaki da hulan kwano ya fasa gilashin masallaci rike da bindigogi kuma ya fara harbi.

Kawai sai mutanen da ke cikin masallacin suka rufeshi da duka har suka samu damar dakileshi kuma suka mikashi ga hukuma.

KU KARANTA: Manufarmu itace samawa El-Rufa'i bashin bankin duniya $350m - Dan majalisar wakilai

Jama'a sun siffata dattijon da ya dakile wannan matashi a matsayin babban jarumi duk da cewa ya samu raunuka sakamakon hakan.

Dattijon mai suna Rafiq ya bayyana godiyarsa ga al'umma bisa goyon bayan da suka bashi. Ya ce yayinda yake rike da matashin da ya kawo hari masallaci, wani masallacin, Mohammed Iqbal, ya rotsa masa kai.

Irin wannan abu ya faru a kasar New Zealand ranar 15 ga watan Maris, 2019 inda matashi ya harbe masallata 50 cikin masallatai biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel