Tambuwal ya raba ‘Goron Sallah’ naira miliyan 70 ga alhazai 3,496

Tambuwal ya raba ‘Goron Sallah’ naira miliyan 70 ga alhazai 3,496

Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya rabar da naira miliyan 70 ga alhazan jahar da a yanzu haka suke kasar Saudiyya suna gabatar da ibadun aikin Hajji, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin mataimakin gwamnan jahar Mannir Muhammad Dan’Iya, Aminu Abdullahi Abubakar ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Wanda bai ji bari ba: Saurayi ya murde wuyan budurwarsa a wani gidan holewa

Mataimakin gwamna Dan Iya, wanda shine jagoran alhazan jahar Sakkwato ya mika gaisuwar maigidansa Tambuwal ga alhazan Sakkwato yayin da suke garin Muna a kasar Saudiyya.

“Gwamna Aminu Tambuwal ya amince da biyan kowanne Alhaji da Hajiya Riyal 200, kimanin N24,000 ga dukkanin alhazan jahar guda 3, 496 a matsayin Barka da Sallah domin su samu saukin zama a garin Makkah.

“Gwamnan ya yi haka ne domin tallafa ma alhazai dake neman taimako sakamakon guzurinsu ya fara yin kasa don su samu kudin cin abinci da kuma zirga zirga.” Inji shi.

Mataimakin gwamnan ya nemi mahajjatan dasu jajirce wajen yi ma jahar Sakkwato addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai daurewa, da ma Najeriya gaba daya.

Daga karshe Alhaji Mannir Dan Iya ta baiwa alhazai tabbacin fara jigilarsu zuwa gida Najeriya daga ranar 17 ga watan Agusta, kamar yadda hukumar alhazan Najeriya, NAHCON ta tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel