Kisan ‘yan sanda: Ku rika yin tafiya cikin farin kaya, shawarar Buratai ga sojoji

Kisan ‘yan sanda: Ku rika yin tafiya cikin farin kaya, shawarar Buratai ga sojoji

Biyo bayan kisan ‘yan sanda uku da sojojin 93 Battalion ta jihar Taraba su kayi a ranar Talatan da ta gabata, Hafsun sojojin Laftanal Janar Tukur Buratai ya gargadi jami’ansa da su sa ido kwarai wurin mu’amala da ‘yan sanda.

Har ila yau ya shawarci jami’an sojojin wadanda ke kan hanyar tafiye-tafiye da su rika sanya farin kaya a lokutan da suke kan hanya domin gudun sa’insa tsakaninsu da ‘yan sanda.

KU KARANTA:Zakzaky zai tafi kasar Indiya a yau Litinin

Idan baku manta ba, a ranar Talatan da ta gabata ne sojoji suka kashe wasu ‘yan sanda uku wadanda suke dauke da Hamisu Wadume wanda yayi kaurin suna wurin garkuwa da mutane.

Sufeta Mark Ediale, Sajan Usman Danazumi da kuma Sajan Dahiru Musa su ne sojojin suka kashe yayin da suke hanyarsu ta zuwa hedikwatar ‘yan sanda dake Jalingo domin isar da wanda suka kaman.

Har ila yau, sojojin sunyi korafin cewa dalilin da har ya sanya suka budawa jami’an ‘yan sandan wuta shi ne rashin tsayawarsu a check point bayan an tsaidasu. Sai dai kuma hukumar ‘yan sanda tayi watsi da wannan batun na rundunar sojin.

A wata takarda da Hafsun sojin Najeriya ya fitar mai dauke da kwanan watan Juma’a 9 ga watan Agusta, ya ce hukumar ‘yan sanda na fadin kalaman marasa dadi game da sojoji a kan shafukan sada zumunta.

Bugu da kari, a cikin takardar tasa ya ja hankalin dakarun sojin da su lura kwarai musamman a cikin halin tafiya da su sa farin kaya domin guje ma faruwa abu mara kyau a garesu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel