Zakzaky zai tafi kasar Indiya a yau Litinin

Zakzaky zai tafi kasar Indiya a yau Litinin

Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wadda aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakazky zai tashi daga filin jirgin Abuja zuwa Indiya a yau din nan.

El-Zakzaky zai tafi Indiya tare da matarsa Zeenat inda za su nufi Asibitin Medenta dake New Delhi a kasar ta Indiya domin a duba lafiyarsu.

KU KARANTA:‘Yan bindiga sun yi awon gaba da jagoran PDP a Kogi

Wata majiyar IMN dake Kaduna ce ta sanar da wakilin Daily Trust wannan labarin inda ta ce, jagoran na IMN yanzu haka yana Abuja tare da jami’an tsaron DSS inda yake jiran tashinsu zuwa Indiya a wani karamin jirgin sama.

Idan baku manta ba dai, wata babbar kotun Kaduna ce ta bai wa Zakzaky da matarsa izinin tafiya Indiya domin a duba lafiyar jikinsu.

A yanzu haka kotun ta basu izinin tafiyar ne inda za a cigaba da shari’arsu da zarar sun dawo daga asibitin.

Haka zalika, gwamnatin jihar Kaduna ta kawo korafinta mai dauke da sharudda 7 da take neman a gindayawa Zakzaky kafin a barshi yayi wannan tafiya.

Abinda kawai har yanzu bamu samu cikakken bayani a kai ba shi ne ko Zakzaky ya cika dukkanin sharuddan gwamnatin jihar Kaduna 7 ko bai cika.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel