Ekiti: Masu sarautar gargajiya su na karar Gwamna Fayemi

Ekiti: Masu sarautar gargajiya su na karar Gwamna Fayemi

Mun ji cewa manyan mutane 16 da ke cikin majalisar Sarakunan jihar Ekiti sun kai gwamna Kayode Fayemi kara gaban kotu a game da nadin da ya yi na shugaban majalisar Sarakuna.

Wadannan manyan kasa da su ka kira kansu da ‘Pelupelu Obas’ sun yi tir da yadda mai girma gwamna Dr. Kayode Fayemi ya zakulo wanda bai cikin su a matsayin shugaban majalisar Sarakuna.

A cewar Sarakunan na Ekiti, gwamnatin jihar ta sabawa dokar sarauta wajen nada Mai martaba Alawe na kasar Ilawe-Ekiti watau Sarki Adebanji Alabi, a kan kujerar shugaban Sarakunan kaf kasar Ekiti.

Daga cikin wadanda wannan Sarakuna su ka hada a wannan kara gaban kotu, akwai Kwamsihinan shari’a wanda shi ne babban Lauyan gwamnatin Ekiti, Wale Fapohunda da kuma Sarkin Oye.

KU KARANTA: Sarkin Daura ya yi wa Shugaban kasa Buhari addu’o’in Sallah

Lauya Dr B. A. M. Ajibade, shi ne ya shigar da wannan kara a kotu a madadin wadannan Sarakuna 16 da su ke da ja da gwamnatu. Ajibade ya na so kotu ta takawa gwamnan burki a game da nadin da ya yi.

Sarakunan sun fadawa kotu cewa su kadai ne asalin masu kasa na yanka a jihar Ekiti don haka su ka ce nada ‘Alademerindinlogun’ a matsayin shugabansu ya sabawa doka tare da wulakanta gadon mulki.

Bayan haka manyan masu kasar sun fadawa gwamnatin jihar cewa ba za su halarci bikin rantsar da Sarki Adebanji Alabi a matsayin shugaba ba, sannan kuma su ka ce, ba za su taba zuwa taron da ya kira ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel