‘Yan bindiga sun yi awon gaba da jagoran PDP a Kogi

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da jagoran PDP a Kogi

-'Yan bindiga sun sace shugaban PDP na Okene Musa Adelabu

-'Yan bindigan sun sace dan siyasar ne a gidansa dake Okene a daren Asabar misalin karfe dayan dare

-Hukumar 'yan sanda ta ce bata samu rahoton satar Adelabu ba a don haka ita maganar ba ta gabanta a halin yanzu

Wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji sun dauke shugaban jam’iyyar PDP na garin Okene dake jihar Kogi, wato Musa Adelabu.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar baki daya Sam Uhuotu wanda ya shaidawa manema labarai wannan labari a ranar Lahadi ya ce dauke Adelabu alamace mai nuna jihar Kogi babu tsaro ko kadan.

KU KARANTA:Zaben Kogi: Babu wanda zan hana tsayawa takara – Bello

Shugaban ya ce, ‘yan bindigan sanye suke da kakin sojoji a lokacin da suka dira gidan Musa kana suka yi gaba da shi misalin karfe daya na daren Asabar.

Ya bayanna lamarin a matsayin abu mara dadi da kuma ban takaici. Har ila yau, shugaban PDP ya koka game da yadda jami’an tsaro ke muzgunawa ‘yan jam’iyyarsu a jihar cikin ‘yan kwanakin nan.

Haka zalika, ya bayyanawa ‘yan jarida cewa a daidai lokacin daukar wannan rahoton ba su samu labarin wurin da Adelabu yake ba. Saboda ‘yan bindiga ba su kira waya ba.

A bangare guda kuwa, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar William Aya ya ce hukumarsu ta ‘yan sanda ba ta da labarin satar Adelabu saboda babu wanda ya kawo masu rahoton abinda ya faru.

“ Idan muka samu rahoton abu makamancin wannan ne muke daukan mataki akai, amma yanzu da ba a kawo mana rahoto ba wannan ba matsala ba ce a gabanmu.” Inji Aya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel