Manufarmu itace samawa El-Rufa'i bashin bankin duniya $350m - Dan majalisar wakilai

Manufarmu itace samawa El-Rufa'i bashin bankin duniya $350m - Dan majalisar wakilai

Wani dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltan mazabar Kachia/Kagarko na jihar Kaduna, Gabriel Saleh Zock, ya ce babbar manufar dukkan mambobin majalisar wakilai daga jihar Kaduna shine tabbatar da cewa gwamnatin jihar karkashin Nasir El-Rufa'i ta samu bashin $350m na bankin duniya.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne ga manema labarai a jihar Kaduna inda ya ce babu wani nasara da zai samu ba tare da dukiya ba.

Za ku tuna cewa a majalisar da ta shude, gwamna El-Rufa'i ya bukaci bashin bankin duniya amma sanatocin jihar karkashin jagorancin Sanata Shehu Sani suka hanashi.

KU KARANTA: Kisan yan sanda 3: An damke babban jami'in soja da ya jagoranci harin

A cewar Gabriel Zock, a yanzu dukkan yan majalisar sun hada kai domin tabbatar da cewa an samu wannan bashi.

"Manufarmu itace tabbatar da cewa mun wakilci Kaduna yadda ya kamata. Za mu tabbatar da cewa munyi duk abinda zai kawo cigaba jihar Kaduna."

"Muna majalisar dokokin tarayya kuma tunda al'ummar jihar Kaduna suka aikamu majalisar, duk abinda gwamnan jihar Nasir El-Rufa'i da mutan jihar Kaduna ke so zamuyi musu."

"Babu abinda za'a iya yi ba tare da kudi ba. Muna sane cewa za'a karbi bashin kuma ba zamu biya Riba ba. Tabbas mun sani irin abun da wannan kud zai yiwa jihar Kaduna."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel