Zaben Kogi: Babu wanda zan hana tsayawa takara – Bello

Zaben Kogi: Babu wanda zan hana tsayawa takara – Bello

-Gwamnan Kogi ya ba al'ummar jihar Kogi tabbacin tsaro a lokacin zaben gwamnan jihar dake tafe a watan Nuwamba

-Gwamna Bello yayi wannan jawabin ne ga manema labari bayan ya idar da sallar idi ranar Lahadi a gari Okene

-A cewar Bello tsare rayuwa da dukiyar jama'a shi ne muradin gwamnatinsa don haka abokan takarsa ma ba za a waresu ba

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bada tabbacin tsaro ga al’ummar jihar a bisa zaben dake tafe na ranar 16 ga watan Nuwamba, 2019.

Gwamna Bello wanda ya tattaunawa da manema labarai jiya Lahadi bayan idar da sallar idi a garinsa na Okene, ya yi kira ga ‘yan takara tare da magoya bayansu da su cigaba da gudanar da kamfe cikin tsanaki.

KU KARANTA:Babbar Sallah: Manyan Sarakunan Arewa sun aika da muhimman sakonni

Ya kuma yi gargadi da cewa, duk wanda ya kawo rikici a lokaci zaben ko bayan an kammala zaben zai dandana kudarsa.

Har ila yau, gwamnan ya yi kira ga magoya bayansa da cewa kada su riki abokan takararsa a matsayin masu laifi dalilin tsayawarsu takarar gwamnan. Inda ya kara da cewa haka dimokuradiyya ta gada kowa na da ‘yancin nuna ra’ayinsa a fili.

Bello ya ce: “ Wadanda ke kalubalantar takarata a zaben fidda gwanin APC dake tafe za a basu damar yin takara.

“ A matsayin gwamnatinmu na wadda ta san abinda take yi, tsare rayuka da dukiyoyi jama’a shi ne burinmu kuma dukkanin ‘yan takarar babu wanda za a kebe.”

A karshe ya gargadi wasu manyan kasar nan da su guji kushe Shugaba Buhari saboda shugaban kasa na iya bakin kokarinsa cikin harkokin kasar nan, a don haka goyon bayan ‘yan Najeriya yake bukata domin samun nasara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel