Kisan yan sanda 3: An damke babban jami'in soja da ya jagoranci harin

Kisan yan sanda 3: An damke babban jami'in soja da ya jagoranci harin

Sakamakon kisan jami'an yan sandan rundunar IRT uku da sojoji suka kashe a garin Ibbi na jihar Taraba, domin tsiratar da wani mai garkuwa da mutane, Alhaji Hamisu, an damke babban jami'in sojan da ya bada umurnin kai harin.

Amma wata majiya daga gidan soja ta bayyana cewa kawai an gayyaci kyaftin din ne saboda ana zargin shi ya bada umurnin kashe yan sandan.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa kyaftin din ya umurci jami'an sojin su kashe dukkan yan sandan da ke cikin motar kuma su saki Alhaji Hamisu Bala Wadume, da aka damke.

A cewar majiyar: "Abokan aikinmu (Yan sanda) sun gaisa da sojojin a karon farko kafin kyaftin ya bada umurnin harbesu."

A bangare guda, Jami'an Rundunar 'Yan sandan Najeriya sun dira garin Ibbi bayan kashe jami'ansu uku da wani farin hula daya da sojoji su ka yi a titin da ya rantsa garin zuwa Wukari.

Daily Trust ta ruwaito cewa jami'an 'yan sandan da suka tafi garin sun kama mutane da yawa.

'Yan sandan sun tafi garin ne domin farautar wani da ake zargi da laifin garkuwa da mutane mai suna Alhaji Hamisu Wadumi da ya tsere a dai-dai wurin da aka kashe 'yan sandan uku da faran hula daya.

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa mataimakin kwamishinan 'Yan sanda Abba Kyari ne ya jagoranci tawagar 'yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel