Miyagu yan bindiga sun kaddamar da farmaki a wata jami’ar Najeriya

Miyagu yan bindiga sun kaddamar da farmaki a wata jami’ar Najeriya

Wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a ranar babbar Sallah a wata jami’ar Najeriya, jami’ar Ibada dake jahar Oyo, inda suka kutsa kai cikin dakunan kwanan dalibai suka tarwatsasu.

Rahotanni sun tabbatar da sanyin safiyar Lahadi, 11 ga watan Agusta ne yan bindigan suka kai farmaki cikin rukunin dakunan kwana da aka sanya ma sunan Abdulsalami Abubakar wanda ya kunshi dakunan maza da na mata.

KU KARANTA: Babbar Sallah: Manyan Sarakunan Arewa sun aika da muhimman sakonni

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa da misalin karfe 2 na dare ne yan bindiga suka shiga dakunan, bayan sun yi amfani da adda wajen karya kofofin shiga harabar dakunan, sa’annan suka fara bi daki daki suna kwashe wayoyin hannu, kwamfuta da kudade.

Daraktan sashin watsa labaru na jami’ar, Tunji Oladejo ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace jami’ar Ibadan na fuskantar matsalolin tsaro kamar yadda ake fama dashi a Najeriya gaba daya, amma suna iya kokarinsu wajen shawo kan matsalar.

Mista Oladejo ya bayyana cewa hukumar jami’ar ta dauki nauyin kulawa da daliban da suka jikkata a sanadiyyar harin, wanda tuni ta garzaya dasu zuwa babban asibitin koyarwa na jami’ar domin samun ingantaccen kulawa.

“Rukunin dakunan Abdulsalami Abubakar sun kunshi Maza da Mata ne, kuma wadanda suka aikata wannan fashi da makami sun san wajen da kyau, domin kuwa basu shiga dakunan Maza ba, a yanzu haka mun kaddamar da cikakken bincike don gano yadda hakan ta kasance, domin a kiyayi gaba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel