Tabbatar da zaman lafiya da sauran sakonni 6 da Buhari ya yi a jawabansa na goro Sallah

Tabbatar da zaman lafiya da sauran sakonni 6 da Buhari ya yi a jawabansa na goro Sallah

A yayin da mabiya addinin Islama ke tururuwa wajen gudanar da bikin babbar Sallah a yau Lahadi, 11 ga watan Agustan 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gabatar da sakonninsa na taya murna.

Shugaban kasa ya gabatar da sakonninsa na goron Sallah tun a ranar Asabar, 10 ga watan Agustan 2019, wanda ya yi daidai da ranar hawan Arfa, 10 ga watan Zhul Hijja bayan hijirar fiyayyen halitta daga birnin Makkah zuwa Madinah.

Shugaban kasar yayin hudubarsa ta goron sallah ga daukacin al'ummar Musulmi, ya gargade su akan zaman lafiya tare da cewar tsauttsauran ra'ayi mai cike da tashin hankali, na daya daga cikin miyagun kalubale da addinin Islama ke fuskanta a yanzu.

1. Musulunci tubali zaman lafiya

Shugaban kasa Buhari ya kirayi musulmi da su kauracewa dukkanin wata tarzoma da tashin-tashina domin kuwa addinin su ya horar da su a kan wanzar da zaman lafiya. Ya nemi da su nesanta kawunan su daga dukkanin wani mummunan lamari da zai haddasa batanci ga addinin Islama.

2. Tsattsauran ra'ayi mai haddasa tarzoma

Shugaba Buhari ya ce tsattsauran ra'ayi mai tattare da tayar da husuma na daya daga cikin manyan kalubale da addinin musulunci ke fuskanta a doron kasa. Ya shawarci al'ummar Najeriya da su nesanta kawunan su daga koyarwar duk wasu masu akida ta tsattsauran ra'ayi mai

3. Ku kare 'ya'yan ku daga masu akidar tsattsauran ra'ayi

Shugaban kasa Buhari ya gargadi iyaye da su sanya idanun lura a kan 'ya'yayen su tare da horar da su wajen nesanta daga masu akidar ra'ayin rikau.

4. Boko Haram ta buwaya a sanadiyar rashin nuna damuwa kan illar da tsattsauran ra'ayi zai haifar

Shugaban kasar ya ce ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ya ta'azzara ne a sanadiyar halin ko in kula da musulmai suka yiwa masu tsattsauran ra'ayi da ke da tasiri wajen yaudarar masu nakasun fahimta.

5. Za a magance ta'addanci da sauran miyagun ababe a Najeriya

Shugaba Buhari ya sake bai wa 'yan Najeriya tabbacin kawo karshen ta'addanci da miyagun ababe na rashin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a kasar.

KARANTA KUMA: Babbar Sallah: Allah ya albarkaci dukkanin Musulmi a duniya - Goodluck Jonathan

6. An samu tangarda a fagen yaki da ta'addancin Boko Haram

Shugaba Buhari ya ce duk da nasarorin da aka samu a gwamnatinsa wajen kwato dukkanin alkaryar da ta koma hannun 'yan ta'adda, ya ce tabbas dakarun sojin Najeriya sun yi rauni wajen yakar ta'addancin masu tayar da kayar ta Boko Haram.

7. Bai wa 'yan Najeriya kariya ya zama wajibi

Shugaban kasa Buhari ya ce samar da tsaro da bai wa 'yan Najeriya kariya ya zama wajibi da rataya a wuyansa da kuma na dakarun sojin Najeriya da aka horas da su tare da mallaka masu makama.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel