Babbar Sallah: Allah ya albarkaci dukkanin Musulmi a duniya - Goodluck Jonathan

Babbar Sallah: Allah ya albarkaci dukkanin Musulmi a duniya - Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, cikin sakon sa na goron sallah da ya yada a shafinsa na zauren sada zumunta, ya taya daukacin musulmi murnar babbar Sallah da ake gudanarwa a yau Lahadi, 11 ga watan Zhul Hijja, 1440.

Cikin sakon da rubuta a shafin sa na Facebook a ranar 1 ga watan Agsutan 2019, tsohon shugaban kasa bayan taya musulmi murnar babbar sallah, ya kuma kwarara addu'o'i na musamman a gare su.

Addu'o'i hudu da tsohon shugaban kasar ya yiwa musulmi a wannan babbar rana ta farin cikin sun hadar da;

1. Ya roki Mai Duka da ya tabbatar da duga-dugansu kan imani tare da tsarkake masu imani wajen da riko da gaskiya.

2. Ya nemi Ubangijin Talikai da ya karbi ibadu da kuma sadaukarwa ta dukkanin musulmi a wannan rana.

3. Ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya kawo masu hasken rahama ta farin ciki gami da jin dadi.

4. Ya kuma roki Wanda baya da nan ballantana ya inanta, kuma baya da can ballanta ya icanta, a kan ya jibinci lamarin musulmi wajen mamaye zukatansu da kyakkyawan zato.

Ga sakon tsohon shugaban kasar kamar haka:

KARANTA KUMA: Tallafin man fetur ya lashe N308bn cikin watanni uku a Najeriya

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, yayin watsa sakonnin sa na taya murnar babbar sallah ga daukacin musulmi, ya nemi da su bi tafarkin koyarwar Annabi Ibrahim (A.S).

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel