'Yan sanda sun kama mutumin da ya yi wa yarinya mai shekaru 10 ciki a IDP

'Yan sanda sun kama mutumin da ya yi wa yarinya mai shekaru 10 ciki a IDP

'Yan sanda a jihar Benuwe sun yi bajakolin masu laifi 15 da suka kama a jihar sakamakon aikata laifuka daban-daban a sassan jihar.

Daga cikin masu laifin da aka yi bajakolinsu akwai wani matashi, Terna Taga, mai shekaru 18, da ya yi wa wata yarinya, mai shekaru 10 da ke sansanin 'yan gudun hijira, ciki.

Yarinyar ma ta haifi diya mace ranar Asabar, 4 ga watan Agusta.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa Taga ya amsa da bakinsa shine ya yi wa yarinyar ciki, ya kara da cewa ya taba kwanciya da yarinyar sau biyu, a saboda haka ya amince cewa shine uban jaririyar da yarinyar ta haifa.

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewa yarinyar ta haihu ne a wani babban asibitin garin Makurdi, kamar yadda wani mutumi mai suna Ukan Kurugh ya tabbatar, wanda yace shi da wasu mutane suka kai yarinyar asibiti.

DUBA WANNAN: Da sauran tsalle: Ganduje ya umarci Hakimai su kaurace wa sarki Sanusi II

Bayan na samu labarin nakudar yarinyar, sai muka tafi da wasu mutane muka tafi babban asibitin gwamnati Makurdi inda muka nemi su bamu izini mu dauketa daga nan, sai muka kai ta asibitin Foundation dake garin Makurdi domin samun isashshen kulawa.

“Da misalin karfe 1 na dare muka dauketa daga babban asibitin gwamnati zuwa asibitin Faoundation, duka duka bai wuce awa daya da kaita asibitin ba Mesenengen ta haihu, inda ta haifi jaririya mace wanda nauyinta ya kai kilo 2:5, bayan an yi mata tiyata.” Inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel