Da sauran tsalle: Ganduje ya umarci Hakimai su kaurace wa sarki Sanusi II

Da sauran tsalle: Ganduje ya umarci Hakimai su kaurace wa sarki Sanusi II

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci hakimai 36 daga cikin 44 da ke jihar Kano da su kaurace wa hawan Daushe da ake yi a cikin birnin Kano.

Umarnin gwamnatin jihar ya saba wa sanarwar da fadar masarautar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta fitar, inda ta gayyaci dukkan hakiman jihar Kano da su halarci hawan Daushe, wanda aka saba yi kwana daya da Sallah.

A ranar 8 ga watan Mayu ne, gwamna ganduje ya saka hannu a kan wata sabuwar dokar majalisar jihar Kano wacce ta kirkiri karin wasu saraku masu daraja ta farko a Rano, Bichi, Karaye da Gaya.

Wasu manyan masu rike da mukaman sarauta sun garzaya kotu tare da neman ta dakatar da Ganduje daga batun nada sabbin sarakuna a sabbin masarautun da ya kirkira.

Ana ganin gwamna Ganduje ya kirkiri sabbin masarautun ne domin rage karfin da masarautar Kano keda shi.

A wani jawabi da, Abba Anwar, kakakin gwamna Ganduje ya fitar ranar Lahadi, ya bukaci Hakiman da su yi watsi da umarnin sarkin Kano na su zo birnin Kano domin gudanar da hawa tare da umartarsu da su gudanar da hawa a karkashin sabbin masarautunsu.

DUBA WANNAN: Sallah: Buhari ya yanka ragonsa na layya a Daura (Bidiyo da hoto)

"Sakamakon wata sanarwa da ke yawo a kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta a kan cewa ana umartar dukkan hakiman Kano su halarci 'Hawan Daushe' a masarautar Kano, gwamnatin jihar Kano na umartar dukkan hakiman Kano da su gudanar da bukukuwan hawan Sallah a karkashin masarautunsu.

"Gwamnatin jihar Kano na umartar hakiman dake karkashin masarautar Bichi da su halarci hawan Daushe a masarautarsu tare da sarkinsu, Alhaji Aminu Ado Bayero. Hakimai daga masarautar Rano zasu gudabar da hawan Daushe tare da sarkinsu mai daraja ta daya, Alhaji Tafida Abubakar (Autan Bawo).

"Dukkan hakimai daga masarautar Karaye zasu gudanar da hawan daushe tare da sarkinsu mai daraja ta daya, Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar, yayin da hakimai daga masarautar Gaya zasu gudanar da nasu hawan tare da sarkinsu mai daraja ta daya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, su kuma hakiman dake karkashin masarautar Kano zasu gudanar da hawansu tare da sarkinsu mai daraja ta daya, Muhammadu Sanusi II.

"Yayin da gwamnatin Kano ke umartar hakimai da su yi biyayya ga wannan umarni, gwamnati na yiwa dukkan Musulmai barka da Sallah da fatan za a yi bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel