Sojojin Najeriya sun kaddamar da wata cibiyar samun bayanai a jihar Filato

Sojojin Najeriya sun kaddamar da wata cibiyar samun bayanai a jihar Filato

Mun samu labari cewa Dakarun Jami’an tsaron Najeriya na Operation Safe Heaven da ke karkashin Manjo-Janar Augustine Agundu sun kaddamar da wata cibiya a cikin jihar Filato.

Sojojin na Operation Safe Haven sun bude wannan cibiya ne domin ganin an yi bukukuwan babbar sallah cikin koshin lafiya a yankin. Wani babban Jami’in sojin ya bayyana wannan a Jos.

Kanal Emmanuel Karau a lokacin da ya ke magana da yawun Dakarun Sojin ya bayyana cewa an kafa wannan cibiya ne domin samun bayanai game da duk abubuwan da ke faruwa a shiyyar.

A daidai lokacin da a ke bukukuwan idi, Emmanuel Karau ya ke cewa za a yi amfani da wannan cibiya wajen bibiyen abubuwan da ke gudana a yankin Filato da ke Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Kanal Karau ya kuma fadawa Manema labarai cewa wannan cibiya za ta samu wakilci daga duk wani bangare na jami’an tsaro da ke fadin jihar. Cibiyar za ta yi aiki ne na tsawon kwanaki uku.

KU KARANTA: Yadda Dakarun DSS su ka shiga har daki sun kama Sowore

Hakan na nufin ‘yan sanda da Takwarorinsu za su shiga cikin harkar kula da wannan cibiya ta musamman. Babban Sojan ya ce yanzu lokaci ne da jami’an tsaro ke bukatar samun bayanai.

“Cibiyar za ta yi aiki ne domin samun bayanai tare da sa-idanu a game da abubuwan da ke aukuwa a yankunan mu a lokacin bikin sallah. Yanzu lokaci ne da samun bayanai zai yi wa jami’an tsaro amfani.” Inji Karau

Jami’in Sojojin kasar ya bayyana cewa sun dauki makonni biyu su na shiryawa bikin sallar a Najeriya. Karau ya ce hakan ya zama dole ne bayan Idi ta fado a Ranar Lahadi da a ke zuwa coci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel