Hajjin bana: Aisha Buhari ta jajjefi Shaidan (Hotuna, bidiyo)

Hajjin bana: Aisha Buhari ta jajjefi Shaidan (Hotuna, bidiyo)

- Uwargidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta saka faifan bidiyon ta na jifan shaidan a shafinta na dandalin sada zumunta 'Instagram'

- Jifan Shaidan na daga cikin aiyukan Hajji da ake gudanar wa ranar Arafat

- A cikin faifan bidiyon, an ga Aisha na daukan hoge domin jifan Shaidan kamar yadda duk sauran maniyyata ke yi

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta saka faifan bidiyonta na jifan Shaidan a shafinta da dandalin sada zumunta (Instagram).

Jifan Shaidan na daga cikin aiyukan Hajji da maniyyata ke gudanar wa a Makkah bayan sun sauko daga hawan Arafat.

A cikin faifan bidyon, an ga Aisha na addu'a tare da sauran maniyyata kafin ta jefi bangon da ake jifan Shaidan.

A ranar Arafat ne aka samu barkewar ruwa kamar da bakin kwarya yayin da Alhazai kimanin miliyan 1.8 suka tattara a dutsen Arafat a birnin Makkah.

An fara mamakon ruwan saman ne da misalin karfe 2:30 na rana, kimanin awa daya bayan masu aikin Hajji sun gabatar da Sallar Azahar da La'asar.

DUBA WANNAN: Sallah: Buhari ya yanka ragonsa na layya a Daura (Hoto, bidiyo)

Zubar ruwan saman ta bayar da mamaki matuka, saboda ba ksafai ake samun saukar ruwan sama a ckin kwanaki biyar da ake gudanar da aiyukan Hajji ba.

Rahotanni sun bayyana cewa yanayin garin Makkah da sauaran biranen kasar Saudiyya ya kai 40` a ma'aunin Celsius, lamarin daku nuna cewa an fusakanci matsanancin zafi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel