Shugaba Buhari ya raba N250, 000, shinkafa, da shanu ga masu NYSC

Shugaba Buhari ya raba N250, 000, shinkafa, da shanu ga masu NYSC

Yanzu nan mu ke samun labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya raba kayan abinci da kyautar kudi ga wasu Matasa masu yi wa kasa hidima watau NYSC a Garin Daura a Katsina.

Shugaban kasar ya bada kyautar wannan kaya ne a gidansa da keUnguwar GRA a Daura a matsayin goron sallah na bikin babbar idi da a ke yi yau, Lahadi 11 ga Watan Agusta, 2019.

Muhammadu Buhari da kuma babban Bakonsa watau shugaban kasar Guinea, Alpha Conde, wanda ya zo garin Daura domin ya yi sallah tare da shugaban Najeriya ne su ka gana da Matasan.

A na sa jawabin wanda wani tafinta ya rika fassarawa wadanda su ka fito daga wasu Garuruwa, shugaban kasar ya yabawa wannan tsari na NYSC wanda ya ce ya ke hada kan jama’a a kasar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yanka ragon layya a Garin Daura

“NYSC zai sa ku san wurare sannan ku samu ilmi a game da sauran bangarorin kasar. NYSC da aikin Soja ko ‘Dan sanda ne kurum ke hada jama'an kasar a wuri guda.” Inji Shugaba Buhari.

Shugaba Alpha Conde ya yi jawabi ga wadannan Matasa da ke bautawa kasarsu inda ya fadakar da su cewa ya kamata su sa kishin Najeriya a gaba kafin su yi maganar kabilar da su ka fito.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya ke cewa Buhari ya bada kyautar buhunan shinkafa 10 da kuma shanu ga Matasan. Bayan nan kuma an ba su kyautar N250, 000.

Shi ma shugaba Conde na kasar Guinea ya bada na sa kyautar na shanu biyu ga wadanda su ka kawo ziyara wajen shugaban kasar. Yanzu haka a na ta faman bukukuwan babbar idi a Duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel