Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga Mutane su ba ilmi muhimmanci a sakon bikin Idi

Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga Mutane su ba ilmi muhimmanci a sakon bikin Idi

Sarkin Birnin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya yi nasiha ga Iyaye da su koyawa ‘Ya ‘yansu tsoron Allah madaukaki. Mai martaban ya yi wannan wa’adi ne a Ranar bikin babbar Sallah.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II shi ne wanda ya jagoranci sallar idi a Birnin Kano a yau Lahadi, 11 ga Watan Agusta, 2019. An yi sallar ne a filin idi na Kofar Mata da ke cikin Kano.

Mai martaba ya mike bayan sallar idin inda ya yi kira ga Mutanen kasar su dage wajen ganin sun ba ‘Ya ‘yansu ilmi tare da koya masu tsoron Allah domin a samu al’umma mai nagarta a nan gaba.

Sarkin ya jawo hankalin jama’a su zama masu cika alkawuran su. Bayan nan, Fitaccen Sarkin ya yi kira ga mutane su zauna lafiya da juna cikin soyayya da aminci da kuma kwanciyar hankali.

KU KARANTA: Gwamna Sokoto ya yi wa mutanensa nasiha a sakon barka da sallah

A hudubar da a ka yi a filin idin, an fadakar da Musulmai su rika taimakawa marasa karfi kamar yadda fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW ya koyar musamman a irin wannan lokaci.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi sallah a bayan Sarkin inda ya yi jawabi bayan kammala salla. Kwamsihinan ‘yan sanda na Kano, Ahmed Rabi’u ya halarci wannan sallah.

Sauran manyan masu mulkin gargajiya da jami’an gwamnatin jihar Kano da-dama sun yi sallah a bayan Mai martaba Muhammadu Sanusi II a wannan wurin sallah da ke Unguwar Kofar Mata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel