Sallah: Buhari ya yanka ragonsa na layya a Daura

Sallah: Buhari ya yanka ragonsa na layya a Daura

Shugaban kasa, Muhammadi Buhari, ya yanka ragonsa na layya bayan ya gabatar da Idin babban Sallah a mahaifarsa, Daura, jihar Katsina.

Buhari ya yi Sallah ne a masallacin idin 'Kofar Arewa' a garin Daura, tare da shugaban kasar Guinea, Farfesa Alpha Conde, wanda ya kawo masa ziyarsa a ranar jajiberin Sallah, ranar Asabar, domin su yi Idin sallah babba tare.

Tun a yammaci ranar Asabar ne Legit.ng ta kawo muku labarin cewa shugaban kasar Guinea, Farfesa Alpha Conde ya iso jihar Katsina a ranar Asabar, 10 ga watan Augusta domin yin bikin sallah tare da takwararsa na Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari.

Sallah: Buhari ya yanka ragonsa na layya a Daura

Buhari ya yanka ragonsa na layya a Daura
Source: Twitter

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito cewa Shugaba Buhari, Gwamna Aminu Masari, Mai Martaba Alhaji Farouk Umar Farouk da sauran al'ummar Katsina sun masa tarbar ban girma.

DUBA WANNAN: Kisan 'yan sanda 3: Rundunar 'yan sanda ta yi wa rundunar sojin Najeriya tambayoyi 2 masu wuyar amsa

Rahoton ya ce mai magana da yawun shugban kasa Garba Shehu ya ce Shugaba Conde ya zo Najeriya ne don yin bikin babban salla.

Ya yi bayanin cewa Shugaba Conde zai yi sallar Idi tare da Buhari a ranar Lahadi 11 ga watan Augusta kuma daga bisani zai tafi kallon hawan durba a fadar Mai Martaba sarkin Daura, Faruk Umar Faruk.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel