Matasa sun hallaka dan sandan da ya harbe mai juna biyu bisa ga kuskure

Matasa sun hallaka dan sandan da ya harbe mai juna biyu bisa ga kuskure

Wasu fusatattun matasa sun hallaka wani jami'in hukumar yan sanda sakamakon kisan wata tela mai juna biyu da yayi bisa ga kuskure inda suke bin wani mai garkuwa da mutane.

Wannan mumunan abu ya faru a unguwar Agbole na garin Ijegun, karamar hukumar Egbe-Idimu na jihar Legas ranar Juma'a, 9 ga watan Agusta, 2019.

An tattaro cewa matasan sun lallasa wasu yan sanda biyu daban inda suka nemi mafaka a fadar sarkin Ijegun.

Rikicin ya fara ne lokacinda yan sandan sukayi harbin kuskure yayinda suke bin wani mai garkuwa da mutane. Harasashin ya samu wata tela mai suna Bilki cikin shagonsa.

An garzaya da ita asibiti inda ta kwanta dama.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Yan Boko na kan kai hari garin Gubio yanzun nan

Mutuwarta ya tayar da hankulan makwabta da mazauna garin inda suka ce ta yaya yan sanda zasu rika harbi cikin jama'a.

A cewar wani, Damilare Olarenwaju, ya ce yan sandan sun yi harbi ne inda suka san akwai tarin jama'a.

Yace: "Labarin da muka samu shine yan sanda daga ofishin Area M suna harbi yayinda suke bin wani dan ta'adda kuma harsashin a kashe matar. Matasan unguwar suka kashe dan sandan kuma suka raunata abokan aikinsa. Daya daga cikinsu ya sha da kyau inda ya gudu fadar sarki,"

Yayinda akaa tuntubi kakakin hukumar yan sanda, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da wannan faruwa.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel