Dalilin da yasa ban fada ma Osinbajo batun hatsarin jirginsa ba – Adeboye ya yi sabon bayani

Dalilin da yasa ban fada ma Osinbajo batun hatsarin jirginsa ba – Adeboye ya yi sabon bayani

Fasto Enoch Adeboye, Shugaban cocin Redemed Christian Church of God (RCCG), ya yi sabon jawabi game da hatsarin jirgi da Yemi Osinbajo, mataimakin Shugaban kasar Najeriya yayi, a lokacin kamfen din zaben 2019.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Adebayo, wanda yayi Magana yayin da yake wa’azi a wani taro, yace ba zai iya fada ma Osinbajo abunda Allah ya nuna masa ba kafin hatsarin jirgin a watan Fabrairun 2019.

Hatsarin jirgin ya afku ne a Kabba, jihar Kogi kafin zaben Shugaban kasa.

Premium Times ta ruwaito cewa Adeboye yace yana a cikin dakin addu’a lokacin da Allah ya sanar dashi cewa dansa na cikin hatsari.

“Na samu sakon amma ban san yadda zan gabatar masa dashi ba. Yana rangaji akan kamfen din siyasa saboda haka ban san yadda zan dakatar dashi ba.

“Sannan kuma bana so ya tsorata saboda haka na yanke shawarar yi masa addu’a,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Guinea a Daura, suna shirin bikin Sallah tare

Ya bayyana cewa yayi addu’a na tsawon mintuna biyu, yana maimaita “Ya Ubangiji, kare danka,” sau hudu.

Osinbajo ya kasance a wajen taron tare da gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel da takwaransa na jihar Lagas, Jide Sanwo Olu, da kuma Godwin Obaseki na jihar Edo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel