Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Guinea a Daura, suna shirin bikin Sallah tare

Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Guinea a Daura, suna shirin bikin Sallah tare

Shugaban kasar Guinea, Farfesa Alpha Conde, ya isa jihar Katsina a ranar Asabar, 10 ga watan Agusta, yayinda yake shirin bikin babban Sallah tare da takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari.

Conde ya samu tarba na musamman daga shugaba Buhari da al’umman Daura a jihar Katsina, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Rahoton ya kawo inda Malam Garba Shehu, hadimin Buhari, ya bayyana a Auja cewa Shugaba Conde na a Daura domin bikin babban Sallah.

Ya yi bayanin cewa Shugaban kasar da ya kawo ziyara zai halarci Sallar idi tare da Buhari a ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta, sannan za a yi hawan Sallah a fadar sarkin Daura, Faruk Umar Faruk don karrama shi.

Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Guinea a Daura, suna shirin bikin Sallah tare

Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Guinea a Daura, suna shirin bikin Sallah tare
Source: Facebook

Jawabin ya kuma bayyana cewa masarautar Daura za ta nada wa shugaba Conde sarauta.

KU KARANTA KUMA: Na sha zagi kan mayar da naira miliyan 15 da na tsinta – Kofur Umar

Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Guinea a Daura, suna shirin bikin Sallah tare

Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Guinea a Daura, suna shirin bikin Sallah tare
Source: Facebook

Shehu ya bayyana cewa ziyarar Conde zai bayar da damar sake karfafa alaka tsakanin shugabannin biyu da kuma kasashen biyu, sannan za su tattauna akan lamuran da suka shafi duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel