Yadda El-Rufai ya yi tafiyar kilomita 10 a kafa domin rage cinkoson da ya hadu a tsakanin Abuja-Kaduna (Hotuna)

-El-Rufai ya kai dauki wurin da aka kashe direban bus tsakanin Abuja zuwa Kaduna

-Gwamnan ya baro abubuwan da ya tafi yi Abuja ne domin ya halarci wurin da mutane ke cikin halin takura saboda cinkoson da ya auku

-El-Rufai yayi tafiya da kafarsa kimanin kilomita 10 a wurin domin kokarin rage cinkoson matafiyan dake kan hanyar

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Juma’a ya baro birnin Abuja domin ya halarci wurin da aka samu cinkoson ababen hawa kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Yadda El-Rufai ya yi tafiyar kilomita 10 a kafa domin rage cinkoson da ya hadu a tsakanin Abuja-Kaduna (Hotuna)

Yadda El-Rufai ya yi tafiyar kilomita 10 a kafa domin rage cinkoson da ya hadu a tsakanin Abuja-Kaduna (Hotuna)
Source: Twitter

Wannan cinkoson ya faru ne a dalilin kisan wani direban bus da wani jami’in ‘yan sanda yayi a safiyar ranar ta Juma’a kan wannan hanyar.

KU KARANTA:Kada ku raba kan Najeriya, sakon Atiku ga Hausawa, Yarbawa da Inyamurai

Domin nuna bacin rai a kan kisan direban sai direbobin manyan motoci suka dates duk hanyoyin biyu babu shiga babu fita daga garin Kaduna.

Yadda El-Rufai ya yi tafiyar kilomita 10 a kafa domin rage cinkoson da ya hadu a tsakanin Abuja-Kaduna (Hotuna)

Malam Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Shi dai wannan direban da ya gamu da ajalinsa yana kan hanyarsa ne ta zuwa Abuja daga jihar Katsina a lokacin da sandan ya bindige shi har lahira saboda ya hana shi naira dubu daya (N1,000).

Yadda El-Rufai ya yi tafiyar kilomita 10 a kafa domin rage cinkoson da ya hadu a tsakanin Abuja-Kaduna (Hotuna)

Yadda El-Rufai ya yi tafiyar kilomita 10 a kafa domin rage cinkoson da ya hadu a tsakanin Abuja-Kaduna (Hotuna)
Source: Twitter

Rahotanni daga jaridar Daily Nigerian sun kawo mana cewa a lokacin da El-Rufai ya samu labarin abinda ke faruwa bai tsaya wata-wata ba sai ya baro garin Abuja ya nufo Kaduna domin ganewa idonsa abinda ke faruwa.

Yadda El-Rufai ya yi tafiyar kilomita 10 a kafa domin rage cinkoson da ya hadu a tsakanin Abuja-Kaduna (Hotuna)

Yadda El-Rufai ya yi tafiyar kilomita 10 a kafa domin rage cinkoson da ya hadu a tsakanin Abuja-Kaduna (Hotuna)
Source: Twitter

Haka zalika gwamnan ya kwashi tsawon lokaci tsaye a kan hanyar inda ya kasance a wurin tun daga karfe 5:30 na yammacin Juma’a har zuwa karfe 2:30 na safiyar Asabar inda ya tabbatar cewa cinkoson ya tsagaita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel