Da duminsa: Dakarun NAF sun tarwatsa hedkwatan bayar da umurnin 'yan Boko Haram a Dusula

Da duminsa: Dakarun NAF sun tarwatsa hedkwatan bayar da umurnin 'yan Boko Haram a Dusula

Rundunar Sojojin Saman Najeriya, NAF ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole sunyi nasarar tarwatsa wani Cibiyar bayar da Umurni na 'yan Boko Haram da ke Dusula kusa da dajin Sambisa a jihar Borno.

Sojojin sun kai farmakin ne karkashin atisayen Operation Green Sweep III da aka kaddamar domin tarwatsa wasu mafakar 'yan ta'addan da aka gano a Borno.

Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayar da sanarwar cikin jawabin da ya fitar a ranar Asabar a birnin tarayya Abuja inda ya ce a ranar Juma'a aka kai harin.

DUBA WANNAN: Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a

Ibikunle ya ce wannan na daga cikin sabbin hare-hare da rundunar ke kaiwa da nuffin kakabo sauran 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ISWAP da su kayi saura a yankin ne Arewa maso Gabashin Najeriya.

"Jiragen yaki kirar Alfa Jet guda uku ne aka yi amfani da su wurin leken asiri domin tabbatar da inda mafakar 'yan ta'adan ya ke.

"An tarwatsa dukkan gine-ginen da ke cibiyar bayar da umurnin da luguden wutan da akayi yayin da an kuma kashe 'yan ta'adda da dama da ke wurin.

"An kuma bi sahun tsirarun wadanda suka tsira daga harin an kashe su yayin da suke kokarin tserewa," inji Ibikunle.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ta ruwaito cewa Daramola ya ce NAF za ta cigaba da aiki tare da sauran dakarun sojojin kasa a yunkurin ta na ganin bayan 'yan ta'addan daga yankin Arewa maso Gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel