Kada ku raba kan Najeriya, sakon Atiku ga Hausawa, Yarbawa da Inyamurai

Kada ku raba kan Najeriya, sakon Atiku ga Hausawa, Yarbawa da Inyamurai

-Atiku ya yi kira ga kabilun Najeriya cewa su aje batun raba Najeriya a gefe

-Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP yayi wannan kiran ne a lokaci da yake fatan a gudanar da bikin sallah lafiya ga 'yan Najeriya

-Atiku ya ce Allah ne haliccemu wuri daya cikin hikimarsa don haka rabawar ba tada wani amfani

A yayin da rigingimu ke cigaba da aukuwa a Najeriya wadanda suka hada da rikicin ‘yan tawayen Biyafara masu fafutukar ganin cewa lallai an raba Najeriya, Atiku Abubakar dan takarar PDP na shugaban kasa ya ce Najeriya tsintsiya ce mai madauri guda.

Atiku yayi wannan kiran ne cikin jawabinsa na fatan alheri ga bikin sallah babba dake tafe ranar Lahadi, inda ya ce wannan lokaci ne na nuna kauna da soyayyar juna kuma ana yin yanka ne domin neman kusanci Allah da kuma hadin kan al’umma.

KU KARANTA:Babbar sallah: Gwamnan Zamfara ya yiwa ‘yan fursuna 150 afuwa

Idan baku manta ba shugaban ‘yan tawayen Biyafara Nnamdi Kanu ya dade yana neman gwamnatin Buhari da ta cire bangaren Inyamurai daga cikin Najeriya.

Kanu ya bayyana gwamnatin tarayya a matsayin mai nuna son kai a bangare guda inda ta fita batu yankinsu na Igbo. Kalaman da ya cigaba da yadawa game da gwamnati kan cewa lallai sai ta ciresu daga Najeriya ya janyo an haramta ayyukan kungiyar.

Har ila yau, Atiku ya yi kira ga ‘yan Najeriya da cewa su kasance tsintsiya madaurinki guda saboda Allah kadai ya san hikimar da ta sanya yayi mu tare wuri daya.

Atiku yayi jawabi mai tsawo wanda a cikinsa ne yayi kira ga ‘yan Najeriya cewa suyi amfani da irin wadannan lokutan na bikin sallah domin yiwa kasarsu addu’a samun zaman lafiya mai dorewa.

Ya sake yin kira ga ‘yan Najeriya cewa kada su bari bambancin addini ko yare ya shiga tsakaninsu saboda Allah ne cikin hikimarsa ya halicci yan Najeriya a wuri daya. A don haka tunanin raba Najeriya ba naku bane, kamar yadda dan takarar shugaban kasan ya fadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel