Takardun bogi: Jami'ar Bayero ta kori dalibanta 24

Takardun bogi: Jami'ar Bayero ta kori dalibanta 24

An kori daliban Jami'ar Bayero ta Kano, BUK guda 24 mafi yawancinsu 'yan ajin karshe daga jami'ar bayan an gano sun gabatar da takardun karatun bogi yayin shiga jami'ar tun da farko.

Sanarwar ta fito ne daga mai magana da yawun jami'ar, Lamara Garba da ya ce mahukunta makarantar sun amince da korar daliban ne yayin taron majalisar jami'ar karo na 374 da aka gudanar ranar Laraba 31 ga watan Yulin 2019.

Ya kara da cewa an kori dalibai shida ne saboda sun gabatar da sakamakon bogi na kammala makarantunsu na baya yayin da wani dalibi an kore shi ne saboda amfani da sakamakon jarrabawar NECO da aka soke.

DUBA WANNAN: Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a

Sanarwar ta kuma ce za a sake gayyato dalibai 18 domin su gurfana gaban kwamitin majalisar jami'ar kan tantance wadanda ke shiga jami'ar domin basu damar kare kansu.

Kazalika, sanarwar ta ce Direktan sashin kula da daukan dalibai da addana bayanansu, DEAR, Amina Umar Abdullahi tayi bayanin cewa an kori daliban ne saboda rahoton da kwamitin majalisar jami'ar ta fitar kan saba wasu ka'idojin daukan dalibai.

Ta ce laifin da daliban da aka kora suka aikata ya saba wa sashi na 3.6 da 3.8(a) na DEAR.

Kididigan daliban da aka kora ya nuna cewa 10 daga cikinsu 'yan tsangayar koyar aikin malanta ne, tara kuma daga tsangayar kimiyyar nazarin hallayar 'yan adam sai kuma dalbai daya daga tsangayoyin koyan karatun lauya, Kimiyya, Aikin Injiniya, Zane da kuma Nazarin karatun addinin musulunci.

Ta ce jami'an za ta cigaba da tantance takardun dukkan daliban jami'ar don tabbatar da cewa sun cika dukkan ka'idojin daukansu aiki a jami'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel