Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)

Kimanin mutum miliyan daya ne suka shiga mawuyacin hali a yankin kasar Ingila da Wales sakamakon daukewar lantarki wadda ta sanya harkokin sufuri da sauran al’amuran yau da kullum suka tsaya cik.

Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)

Birnin Landan
Source: Twitter

Rahotanni daga BBC News sun sanar da mu cewa na’urori biyu ne na ma’aikatar samar da wutar lantarkin suka samu matsala amma an riga da an gyara yanzu haka.

KU KARANTA:Babbar sallah: Hukumar ‘yan sanda ta hana zirgar ababen hawa a Maiduguri

Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)

Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)
Source: Twitter

Kan ayi gyaran an samu yanayin duhu a yankunan Midlands, Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma, Arewa maso Gabas ta Ingila da kuma kasar Wales.

Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)

Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)
Source: Twitter

Daruruwan mutane sun takura a tashar jirgin kasa ta King’s Cross station saboda an soke masu tafiyarsu a dalilin matsalar lantarkin da ta auku. Hatta wutar bisa titi mai rage cinkoson ababen hawa wato traffic lights duk macewa suka yi.

Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)

Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)
Source: Twitter

Kamfanin sufuri na kasar yayi korafi kwarai da gaske a kan wannan al’amarin da ya faru inda ya fadi cewa, “ Matsalar lantarkin yau ta kawo cikasa ga tafiye-tafiye da muka saba yi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel