Yarinya yar shekara 6 ta nuna bajinta inda ta sha gwagwarmaya da wanda yayi garkuwa da ita, sannan ta gane shi

Yarinya yar shekara 6 ta nuna bajinta inda ta sha gwagwarmaya da wanda yayi garkuwa da ita, sannan ta gane shi

Wata yarinya yar shekara shida, Feranmi Bukola ta nuna bajinta inda ta tsallake rijiya da baya daga hannun wanda yayi garkuwa da ita a ranar Alhamis.

An sace Feranmi a gidansu yayinda take bacci a gefen mahaifiyarta, jaridar Daily Trust taruwaito.

Mai laifin, wanda daga bisani Feranmi ta gane kasancewarsa makwabcinsu, ya rufe bakinta ddomin hana ta ihun neman agaji.

Da take bayanin halin da ta shiga, Feranmi tace ta shiga alhini a lokacin da suka fita wajen gidansu sannan mutumin ya ciro wuka domin ya kashe ta.

Tayi ihu, sannan mutumin ya tsere.

Mahaifiyarta, Misis Mary Jumai Samaila Bukola, tace ta tashi daga acci bayan ta jiyo hayaniya a waje.

Tace: “Na tashi da misalin karfe 3:00 na tsakar dare lokacin da na ji kamar hayaniyar wani na son kashe wata dabba, sannan sai na gano cewa ashe yata bata kusa dani. Sai na fita harabar gidan sannan na bude koa, kawai sai na yata na gwagwarmaya da wani mutum a waje.

“Lokaci da na ga wani mutum rike da wuka, sai nayi ihun neman agaji. Sai ya tsere sannan na bishi da duwatsu na dan wani lokaci sannan na dauki yata muka koma cikin gida."

Kawai sai ga shi Feranmi ta gane wanda ya sace ta lokacin da ya ziyarci gidanmu da safe.

KU KARANTA KUMA: Na fi jin dadin aikin hajji cikin talakawa – Gwamnan jihar Bauchi

Feranmi na ganinshi, sai ta saka ihu, sannan ta nuna shi a matsayin mutumin da yayi kokarin sace ta da kuma kashe ta.

Koda aka gabatar mata da sauran mazaje a ofishin yan sandan Area F, Tanke, wannan mutumin dai Feranmi ta nuna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel