EFFC ta fara bincikar gwamnatin Obasanjo kan bannatar da $16bn don samar da lantarki

EFFC ta fara bincikar gwamnatin Obasanjo kan bannatar da $16bn don samar da lantarki

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC ta fara bincike kan shirin samar da wutan lankarki da ya lakume dalar Amurka biliyan 16 a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

An samu banbancin ra'ayi kan takamamen adadin kudin kwangilar samar da wutan lantarkin inda wasu suka ce dala biliyan 16 yayin da wasu suka ce dallar biliyan 13.8 ne.

Rahotanni a daren jiya sun ce akwai yiwuwar hukumar za ta kama wasu daga cikin muhimman wadanda suke da hannu cikin kwangilar da aka cigaba da yin ta har zuwa mulkin marigayin tsohon shugaban kasa Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan.

DUBA WANNAN: Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a

An kuma ruwaito cewa za a gayyaci wasu manyan ma'aikatan gwamnati 18 ciki har da wadanda su kayi murabus da tsaffin ministoci biyu domin amsa tambayoyi kan kwangilar.

Akwai yiwuwar hukumar ta EFCC ta gayyaci wasu manyan jami'an babban bankin kasa, CBN domin suma su amsa tambayoyi.

A karshen watan Yulin 2019 ne majalisar wakilai na tarayya ta cimma matsayar gudanar da bincike kan makuden kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe kan kwangilar na magance matsalar samar da ingantaccen wutan lantarki a kasar.

A baya, tsohuwar gwamnatin na Obasanjo ta ce ta kashe makuden kudi a fannin samar da lantarkin domin samar da karfin wuta kimanin megawatts dubu 40 a shekarar 2020.

Kawo yanzu dai sassan kasar da dama ba shaida wannan alkawarin da aka yi musu na samar da hasken wutar lantarkin isashe ba duba da cewa an kuma ware kudade masu yawa saboda aikin, hakan ya sa gwamnati mai ci yanzu za ta binciki yadda aka kashe kudaden.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel