Zan karbo nasara ta a kotu - Dan takarar gwamnan PDP na jihar Niger

Zan karbo nasara ta a kotu - Dan takarar gwamnan PDP na jihar Niger

- Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben 2019 a jihar Niger, Umar Nasko ya ce yana kyautata zaton kotu za ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben

- Umar Nasko ya bayyana hakan ne yayin da ya ke fitar da sakon taya murnar sallah ga magoya bayansa da sauran al'umma baki daya

- Dan takarar gwamnan ya ce ya yi imani da biyaya ga doka da kuma demokradiyya shi yasa ya garzaya kotun don karbo nasarar da ya ce ya yi a zaben

Umar Nasko, Dan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party na jihar Niger ya ce yana da yakinin cewa kotun sauraron karrarkin zabe za bashi nasarar ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.

A sakon Sallah da ya bawa manema labarai a ranar Juma'a, Nasko ya bukaci al'ummar musulmi su cigaba da yi wa kasa addu'a, inda ya ce rikici da kashe-kashen da aka rika yi bayan zaben 2019 ba zai haifar wa kowa da mai ido ba.

DUBA WANNAN: Matakan da zan dauka kan rikicin Majalisun Bauchi da Edo - Buhari

A cewarsa, "Na yi imani da doka da demokradiyya, wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa ta garzaya kotun sauraron karrarkin zabe domin gurfanar da kara kan magudin zabe da wasu abubuwa da aka yi na saba doka.

"Ina kyautata zaton za a mayar mana da nasarar mu a jihar Nigeri duba da abinda na gani a zaben da ta gaba."

Ya ce, "Maganar gaskiya ita ce bayan babban zaben shekarar 2015 da abokan hammaya su kayi nasara, kowa na tsamanin cewa mun wuce zamanin yin magudin zabe da sauran surkulle amma abin ba ta canza zani ba a zaben 2019 idan aka yi la'akari da kashe-kashe da barazana da hayaniya da suka biyo bayan zaben da ba za su haifar wa kowa da alheri ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel