Babbar sallah: Hukumar ‘yan sanda ta hana zirgar ababen hawa a Maiduguri

Babbar sallah: Hukumar ‘yan sanda ta hana zirgar ababen hawa a Maiduguri

-Hukumar 'yan sanda za ta hana yawo da ababen hawa a Maiduguri ranar sallah

-Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Usman Usmobik ne ya bada wannan sanarwar ranar Juma'a

-A cewar kakakin babu wanda za a bari ya fita da abin hawansa a cikin lokacin da aka sanya dokar matukar ba jami'in tsaro bane shi

Rundunar yan sandan jihar Borno ta ce, ta hana zirga-zirgar ababen hawa a birnin Maiduguri ranar sallah domin a tabbatar da bikin sallar anyi shi cikin kwanciyar hankali.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Usman Usmobik ne ya bada wannan sanarwa a wani zancen da ya fitar ranar Juma’a.

KU KARANTA:Allah mai iko: Wata mata ta haifa ‘yan biyu bayan ta shekara 11 babu haihuwa (Hoto )

Kakakin ya ce yin amfani da wannan tsarin ya kasance dole a garesu saboda tabbatar da an samu tsaro a lokacin gudanar da bukukuwan sallar.

“ Zamu takaita zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 7 na safe zuwa 12:15 na rana a ranar Lahadi 11 ga watan Agusta wadda ita ce ranar idin babbar sallah. Zirga-zirgar ababen hawan ta shafi masu motoci, keke, adaidaita har ma da masu dabbobi.

“ Wadanda kawai ke gudanar da ayyukan hukuma ne za su iya fita a wannan lokacin da abin hawansu.

“ Rundunarmu ta za ta baza jami’ai a fadin jihar nan domin tabbatar da cewa anyi bikin sallah lafiya ba tare da wani firgici ko razani ba.” Inji Usman

Kakakin ya kara da cewa, rundunarsu ta shirya tsaf da jami’anta wadanda za a sanyasu a wurare daban-daban musamman filin sallar idi, wuraren shakatawa, manyan shagunguna da kuma kasuwanni inda ake samun taruwar jama’a musamman a irin lokutan bikin sallah. 

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel