Yanzu-yanzu: Sowore ya garzaya kotu kan izinin da aka bawa DSS na tsare shi na kwanaki 45

Yanzu-yanzu: Sowore ya garzaya kotu kan izinin da aka bawa DSS na tsare shi na kwanaki 45

Madugun zanga-zangar juyin juya hali na RevolutionNow, Omoyele Sowore ya shigar da kara a babban kotun tarayya da ke Abuja inda ya ke neman ayi watsi da umurnin da kotu ta bawa Hukumar 'Yan Sandan Farar Hula, DSS ta rike shi na tsawon kwanaki 45.

Sowore ta hannun lauyansa, Mr Femi Falana ya kallubalinci umurnin dakatar da shi cikin karar da ya shigar a ranar Juma'a inda ya ce kotun ta keta hakkinsa na dan kasa da kundin tsarin mulkin kasa ta bashi.

Ya ce umurnin da kotun ta bayar 'ya hallasta haramtaccen abu' na tsare shi na kwanaki hudu kafin kotun ta bayar da izinin tsare shi a ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Matakan da zan dauka kan rikicin Majalisun Bauchi da Edo - Buhari

Babban kotun tarayya ta yanke hukunci kan bukatar da DSS ta gabatar mata na neman izinin tsare Sowore na tsawon kwanaki 90 domin bincikarsa kan zargin cin amanar kasa

Sai dai Justice Taiwo Taiwo a ranar Alhamis ya bawa hukumar ta DSS izinin tsare Sowore na tsawon kwanaki 45 ne kawai.

An kama Sowore ne a safiyar ranar Asabar bayan ya yi kira ga 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata a ranar Litinin 5 ga watan Augusta domin nuna bakin cikinsu game da irin mummunan salon mulkin gwamnatin.

Hukumar ta DSS ta cigaba da rike Sowore duk da kiraye-kiraye da wasu 'yan Najeriya da kungiyoyin kasa da kasa ke yi na cewa a sake shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel