Jonathan Shugaban kasan ‘jeka na yi ka ne’ – APC

Jonathan Shugaban kasan ‘jeka na yi ka ne’ – APC

-Yekini Nabena ya mayarwa tsohon Shugaban Najeriya martani kan kiran APC jam'iyya maras tasiri a Bayelsa

-Mataimakin sakataren yada labaran APC ya ce Jonathan bai taba lashe zabe ko so daya ba da karfin kuri'u

Mataimakin sakataren yada labaran APC a matakin kasa, Yekini Nabena ya bayyana tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin “ Shugaban kasan jeka na yi ka’ wanda bai taba lashe zabe ko so daya ba.

Mataimakin sakataren yayi wannan maganar ne a lokacin da yake mayar da martani a kan wasu kalaman da tsohon Shugaban ya fadi game da jam’iyyarsa.

KU KARANTA:Dakarun sojin Najeriya sun cikawa Wike aiki na kama Bobrisky

Jonathan ya furta wasu kalamai dangane da jam’iyyar APC a wurin wani taron PDP da aka yi a Yenagoa babban birnin Bayelsa, inda ya ce APC bata da wani tasiri a siyasance a dukkanin matakan jihar.

A nashi bangaren kuwa, Nabena ya mayarwa tsohon shugaban kasan da martani ranar Alhamis a Abuja lokacin da yake hira da ‘yan jarida, inda ya ce a zaben da ya gabata na sanata a mazabar Jonathan dan jam’iyyar APC ne ya lashe kujerar.

Ga abinda Nabena ya fadi a kalamansa: “ Jonathan shugaban kasan jeka na yi ka ne, wanda yake kokari ya kafa tarihi na sake gudanar da zaben shugaban kasa a Bayelsa kamar yadda ya auku a lokacin da yake mulki.

“Bai taba lashe zabe ba ko sa daya. Taimakon jami’an tsaro ne da kuma hukumar zabe a wancan lokacin kawai sai dai ka ji an sanar da sakamakon zabe ana cewa PDP tayi nasara.

“ Ko a zaben da akayi bana Jonathan ya fadi warwas a mazabarsa, saboda dan jam’iyyar APC ne ya lashe kujerar sanatan wannan mazabar. Kaga kuwa dole mutum yayi mamaki wai shin wace jam’iyyar Jonathan ke nufi da cewa ba tada tasiri a Bayelsa.

“ A bayyane take babu irin magudin zaben da zai hana PDP faduwa zaben gwamnan jihar Bayelsa dake tafe nan gaba kadan.” Inji Nabena.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel