Dakarun sojin Najeriya sun cikawa Wike aiki na kama Bobrisky

Dakarun sojin Najeriya sun cikawa Wike aiki na kama Bobrisky

-Sojoji sun kama wanda Gwamna Wike ya sanya a nemo masa tare da kyautar N30m

-Gwamnan jihar Rivers ya tabbatarwa manema labarai cewa Sojoji sun kama Bobrisky kuma zai cika masu alkawarin da ya dauka

-Bobrisky na Gokana wani rikakken dan ta'addane da ya jima ya addabar mutanen jihar Rivers

A cikin kasa da awa 24 da Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya bada sanarwar zai bada tukuicin N30m ga duk wanda ya kamo masa wani qasurgumin dan ta’adda wanda ake kira Bobrisky na Gokana, dakarun sojin Najeriya sun damko wannan mutumin.

Da yake magana a yayin wata ganawa da al’ummar Rumuolumeni a fadar gwamnatin Rivers dake Fatakwal ranar Juma’a, Wike ya yabawa sojojin bisa namijin kokarin da suka yi na kama dan ta’ddan.

KU KARANTA:Hajj 2019: Saudiya ta tanadi motocin karta kwana domin daukan mahajjata marasa lafiya

A cewar gwamnan, “ Sojoji sun kama Bobrisky kuma tabbas zan cika alkawarin da na dauka. Duk wani mai kawo rashin zaman lafiya a jihata a shirye nake da in biya ko nawa domin a kama shi.”

Gwamnan yayi kira ga al’ummar da su zama masu lura a kan abubuwa dake faruwa a yankunansu domin da sun lura da wani sauyi su gaggawar sanar da jami’an tsaro.

Haka zalika, ya sake bayyana yankin na Rumuolumeni a matsayin wurin da yayi kaurin suna wurin aikata muggan laifuka da dama a cikin jihar.

Da yake nasa jawabin wurin taron, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Rivers Mustapha Dandaura ya ce kusan dukkanin garuruwan dake Fatakwal ko wacce na da kungiyar ‘yan asiri. Ya kara da cewa ba aikin jami’an tsaro bane domin su kadai ba za su iya ganin bayan matsalar ba.

Bugu da kari, ya jinjinawa gwamnan jihar bisa gudunmuwar ababen hawa da ya bai wa hukumomin tsaro domin ingantan kula da dukiyoyi da rayukan jama’ar jihar Rivers.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel