Yanzu Yanzu: Buhari ya isa Katsina yana a hanyarsa ya zuwa Daura domin bikin babban Sallah

Yanzu Yanzu: Buhari ya isa Katsina yana a hanyarsa ya zuwa Daura domin bikin babban Sallah

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a, 9 ga watan Agusta ya isa filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua, jihar Katsina a hanyarsa na zuwa Daura, mahaifarsa domin bikin babban sallah da za a yi a ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta.

Shugaban kasar ya isa filin jirgin ne da misalin karfe 5:01 na yamma a cikin jirgin Shugaban kasa mai lambs 001.

Buhari wanda ya samu tarba daga Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da sauran manyan jami’an gwamnati ya bar filin jirgin sama na Katsina da karfe 5:20 na yamma a cikin jirgin Shugaban kasa mai saukar ungulu zuwa Daura.

Shugaban kasar zai sauka a gidansa da ke yankin GRA Daura.

A ranar Lahadi ne Musulman kasar za su bi sahun takwarorinsu a fadin duniya domin bikin babban sallah na wannan shekarar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da belin tsohon Shugaban INEC kan N1bn

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu domin bikin Sallan.

Ana sanya ran Shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka yayin zamansa a Katsina.

Shugaban kasar zai kasance a Katsina har bayan hutun Sallah.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel