Bidiyon yadda Jami’an DSS su ka cafke Yele Sowore har gida kwanaki

Bidiyon yadda Jami’an DSS su ka cafke Yele Sowore har gida kwanaki

Mun samu wani bidiyo da ya ke yawo a gari inda a ka ga yadda Rundunar jami’an tsaro na DSS masu fararen kaya su ka cafke Mista Omoyele Sowore a dakin otel dinsa a makon da ya gabata.

A wannan bidiyo da Sahara Reporters ta fitar a shafinta, an hangi yadda wasu Dakarun DSS su ka duro otel din da Yele Sowore ya ke zaune, inda su ka rika lalube daki zuwa daki su na nemansa.

Wadannan jami’an tsaro sun shigo gidan ne a wasu manyan motoci kirar jeep kamar yadda bidiyon ya nuna. An dauki wannan bidiyo ne daga kananun na’urorin daukan hoto na CCTV na otel din.

A wannan bidiyo an ga yadda wani sanye da gajeren wando ya rika zarya ya na kokarin tare Jami’an tsaron a lokacin da su ke ta faman neman Sowore, bayan nan a ka yi gaba da shi a ka fice.

KU KARANTA: Jam'iyyar AAC ta bankado sirrin Yele Sowore a gaban Duniya

Kwanaki Shugaban jam’iyyar AAC ya ce Yele Sowore ya na zama ne a fitaccen otel dinnan Radisson Blu. Kudin kowane daki a kullum ya na kamawa ne a kan N260, 000 zuwa N270, 000.

Jami’an hukumar DSS sun bayyana dalilin da ya sa su ka yi ram da Jagoran na tafiyar RevolutionNow, Yele Sowore, wanda su ka ce ya na yunkurin kawo tashin-tashina ne a kasar.

Kungiyar kasashen Nahiyar Turai ta EU, ta fito ta yi tir da damke wannan ‘dan gwagwarmaya da a ka yi a Najeriya. Kungiyar ta ce kowa ya na damar ya fito ya fadi abin da ya ga dama a Najeriya.

Ga dai wannan bidiyo nan na yadda a ka yi ram da Yele Sowore har zuwa babban Hedikwatar DSS.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel