Sanata Ahmed Lawan ya taya musulmai murnar babbar Sallah

Sanata Ahmed Lawan ya taya musulmai murnar babbar Sallah

Shugaban majalisar dattawa na Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya taya daukacin al'ummar musulmi murnar bikin babbar sallah ta bana wadda ake gudanarwa a yau Lahadi, 11 ga watan Agustan 2019.

Sanatan Lawal cikin sakon sa na taya murna da ya fito daga bakin mai magana da yawunsa, Ola Awoniyi, ya gargadi musulmi a kan kada su shagala wajen mantawa da muhimmancin bikin babbar Sallah.

Jagoran majalisar tarayyar kasar ya nemi daukacin musulmin Najeriya da su hararo rayuwar Annabi Ibrahim, badadin Ubangijin Talikai, da ya kasance mafarar gudanar da bikin babbar Sallah, wato Sallar Layya.

Ya kuma gargadi dukkanin al'ummar Najeriya da su tsaya tsayin daka wajen sanya tsananin kishi da kuma tabbatar da ci gaban kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Goron Sallah: A guji tsattsauran ra'ayi na tashin hankali - Buhari

Shugaban majalisar dattawan wanda a halin yanzu yana kasar Saudiya wajen sauke farali na aiki Hajji a bana, ya nemi musulman Najeriya da su so junansu wajen tabbatar da hadin kai a yayin da kasar ke warware matsalolin da suka yi mata dabaibayi.

Kazalika, shugaban kasa Muhammadu Buhari, cikin hudubarsa ta taya murnar Sallah ga al'ummar Najeriya, ya nemi da su nesanta kawunansu daga sauraron koyarwar masu tsauttsauran ra'ayi da ke haddasa husuma a tsakanin al'umma.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel