Goron Sallah: A guji tsattsauran ra'ayi na tashin hankali - Buhari

Goron Sallah: A guji tsattsauran ra'ayi na tashin hankali - Buhari

A yayin da mabiya addinin Islama ke tururuwa wajen gudanar da bikin babbar Sallah a yau Lahadi, 11 ga watan Agustan 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi gargadi da a guji tsauttsauran ra'ayi na tashin hankali.

Shugaban kasar yayin hudubarsa ta goron sallah ga daukacin al'ummar Musulmi da ke Najeriya, ya ce tsauttsauran ra'ayi mai cike da tashin hankali, na daya daga cikin miyagun kalubale da addinin Islama ke fuskanta a yanzu.

Buhari cikin hudubarsa ta musamman ya yi hani tare da gargadin mabiya addinin Islama da su nesanta kawunansu wajen sauraron koyarwar masu tsauttsauran ra'ayi na tayar da tarzoma ko kuma mummunar husuma a tsakanin al'umma.

A yayin bibiyar sahun shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan da kuma wasu gwamnonin Najeriya, sun yi kira na neman daukacin al'ummar musulmi da su ci gaba da kwarara addu'o'i na neman kawo karshen ta'addanci da ya yiwa kasar nan dabibayi.

Jerin gwamnonin da suka yi makamancin wannan kira sun hadar da na jihar Oyo, Seye Makinde, gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi, Babajide Sanwo Olu na jihar Legas, Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, da kuma gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola.

KARANTA KUMA: Hatsari: Mutane 20 sun kone kurmus a Bauchi

Kazalika, shugaban kasa Buhari ya tunatar da al'ummar musulmi cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali tambari ne na addinin musulunci da ya wajaba dukkanin mabiyansa su kare martabarsa ta hanyar kauracewa tsattsauran ra'ayi mai cike da tarzoma domin kuwa yin sabanin haka batanci ne ga addinin.

Shugaban kasar wanda ya gabatar da hudubarsa cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya ce gujewa tsauttsauran ra'ayi ita kadai ce mafificiyar hanya ta wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakankanin al'umma.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel