Allah ya kyauta: An rufe hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan wani dan sanda ya harbe wani direban mota har lahira

Allah ya kyauta: An rufe hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan wani dan sanda ya harbe wani direban mota har lahira

- Wani jami'in dan sanda ya harbe wani direban motar haya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, kusa da kamfanin Olam

- Wannan lamari ne ya jawo direbobin motocin haya suka rufe hanyar da motocinsu, inda suka ce baza su bari kowa ya wuce ba sai an dauki matakin wannan kisa da dan sandan yayi

- Kwamishinan jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana cewa suna iya bakin kokarinsu wajen ganin komai ya dawo daidai a hanyar

An rufe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna dalilin wata zanga-zanga da masu motocin haya suke yi bayan wani dan sanda ya kashe wani direban motar haya.

Masu zanga-zangar sunyi amfani da motocinsu sun rufe hanyar, sannan sun bayyana cewa, dan sandan ya kashe marigayin ne a kusa da kamfanin Olam Chicken Feed, yayin da yake kan hanyar Kaduna da safiyar Juma'ar nan.

KU KARANTA: Tirkashi: Wani dan majalisa ya takarkare ya banka tusa a dakin majalisa da ta sanya kowa ficewa daga dakin

Da yake magana game da lamarin, kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce yanzu haka suna yin bakin kokarinsu wurin ganin sun kawo karshen matsalar rufe hanyar.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce: "Muna iya bakin kokarin mu wajen ganin mun kawo karshen rufe hanyar da direbobi suka yi a kusa da kamfanin Olam."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel