Leonard Ezenwa ya fallasa asirin Sowore a rikicin Jam’iyyar AAC

Leonard Ezenwa ya fallasa asirin Sowore a rikicin Jam’iyyar AAC

Yanzu haka a na ta faman rikici a jam’iyyar AAC mai adawa inda har Uwar-jam’iyyar ta sallami ‘dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019 Omoyele Sowore da wasu mutane daga cikin ta.

Mun bi kadin wannan rigima inda mu ka kawo wasu jawabai da shugaban jam’iyyar kuma babban Abokin fadansa watau Mista Leonard Ezenwa ya yi kwanaki inda ya ke sukar ‘dan takarar na sa.

A wani bidiyo da wani Bawan Allah mai suna Gbenga Olorunpomi ya fitar, an ji yadda Leonard Ezenwa ya rika tonawa Yele Sowore asiri kan zargin tafka wasu badakala a cikin tafiyar jam’iyyar AAC.

Leonard Ezenwa ya ke cewa Yele Sowore ya handame wasu makudan kudi akalla Naira miliyan 150 na jam’iyyar AAC da a ka ba su a matsayin gudumuwa a lokacin zaben shugaban kasa da a ka yi.

Shugaban jam’iyyar ta AAC ya ke cewa Sowore ya tare ne na shekara daya a wani katafaren otel mai suna Radisson Blu wanda a duk rana ta Allah a ke biyan fiye da N260, 000 a matsayin kudin daki.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan Legas ya yi magana game da wani zargi a Najeriya

Ezenwa ya kuma fadawa gidan talabijin OAK TV da wasu ‘yan jarida cewa ‘dan takarar na su na shugaban kasar ya rika amfani ne da makudan kudin jam’iyya ya na zagaya Duniya a cikin jirgin sama.

Bayan nan kuma Mista Ezenwa ya fadawa ‘yan jarida cewa Omoyele Sowore ya aikata laifin da ya ke zargin wasu manyan kasar da yi, inda ya ce Sowore ya yi kabebe a kan mukaman jam’iyyar AAC.

A cewar Ezenwa, a matsayin Omoyele Sowore na ‘dan takarar shugaban kasa, ya zama shugaban jam’iyya kuma Ma’aji da kuma Mai magana da yawun bakin ta da karfi da yaji kuma duk a lokaci guda.

A na shi martanin, Yele Sowore ya nanata cewa Leornord Ezenwa ne ya yi awon gaba da kudin jam'iyyar inda ya ke zarginsa da cewa ya na cikin masu hada kai da APC a na yi wa AAC zagon-kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel