Da zafi-zafi: INEC ta sallami kwamishinan zaben Cross River

Da zafi-zafi: INEC ta sallami kwamishinan zaben Cross River

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta sallami kwamishinanta na jihar Cross River, Dr. Frankland Briyai bisa laifin yin amfani da harabar hukumar ba wai don sanar da yin murabus dinsa ba, sai don bayyana sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma neman takara a zaben gwamna da za a gudanar a jihar Bayelsa.

Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da masu zabe na hukumar ne ya bada sanarwar, a wani jawabin da ya gabatar a ranar Juma’a, 9 ga watan Agusta a Abuja.

A cewar hukumar INEC, Dr. Briyai a ranar Alhamis ya gabatar da jawabi ga kafofin yada labarai cewa yayi murabus daga matsayinsa na Kwamishinan INEC daga ranar 8 ga watan Agusta, 2018, sannan kuma cewa ya shiga jam’iyyar siyasa inda yake da ra’ayin tsayawa takara a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba, 2019 wanda za a yi a jihar Bayelsa.

Jawabin yace duk da cewar anyi hakan ne a ofishin hukumar da ke jihar Cross River a Calabar, har yanzu hukumar bata ji wani bayani daga Dr. Briyai akan lamarin ba.

KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan APC ya yi karin haske akan zargin cewa EFCC ta gano N9.9bn da ke da nasaba da shi

Hukumar INEC ta kara da cewa sashi na 306(2) na kundin tsarin mulkin kasar ya nuna cewa duk wani murabus da zai yi daga matsayinsa zai yi tasiri ne bayan hukumar da ta nada shi ta karbi wasikar murabus daga gare shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel