Tsohon gwamnan APC ya yi karin haske akan zargin cewa EFCC ta gano N9.9bn da ke da nasaba da shi

Tsohon gwamnan APC ya yi karin haske akan zargin cewa EFCC ta gano N9.9bn da ke da nasaba da shi

Akinwunmi Ambode, tsohon gwamnan jihar Lagas, ya yi tsokaci akan wani jawabi da aka alakanta ga hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), inda tayi zargin cewa ta daskarar da asusun banki da ke da nasaba dashi.

A cewar Ambode, babu asusunsa da ke dauke da naira biliyan 9.9 balle ma har hukumar EFCC ta daskarar dashi.

Sannan kuma ya kara da cewa a wannan lokaci da ake ciki na bikin Sallah sannan kuma kasancewarsa gwamna a jihar wanda ke da jajircewa da martaba, tarihin da ya kafa tsaftattaciya ce sannan kuma zuciyarsa na cik da farincin damar da ya samu na yiwa jihar aiki nagartacce.

Da yake magana a cikin wani jawabi daga Habib Aruna, hadiminsa, Ambode yace yayinda bai da burin shiga wani lamari da hukumar yaki da rashawa a wannan lokaci, musamman ma a yanzu da babu wata sanarwa tsakaninsa da hukumar akan wanan lamari, yana ganin akwai bukatar yin tsokaci akan abunda yake ganin kagaggen labara ne na masu watsa labarai da suka saki a ranar Talata, 6 ga watan Agusta.

Ambode yayi bayanin cewa asusun da ake Magana akai da babbar kotun taarayya ta bayar da izinin daskararwa mallakar gwamnatin jihar Lagas ne amma ba wai nashi ko na wani ba.

Tsohon gwamnan ya sake a yan Najeriya tabbacin cewa yana nan tare da Shugaban kasa Muhammadi Buhari da kuma manyan iyayen jam’iyya domin ganin an cimma matakin ‘next level’ a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jam’iyyar AAC ta dakatar da Sowore da wasu 28

Ya kuma mika gaisuwar Sallah zuwa ga shugaba Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo; da kuma baban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinuu da kuma mutanen Lagas baki daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel